YA AZUMINSU YA KE !?
YA SADU DA IYALINSA A DAREN RAMADAN, HAR ALFIJIR YA KETO BAI SANI BA:
------------------------------------------------------------
AMSA:
Lokacin da mutum yake saduwa da iyalinsa a daren Ramadan, ba tare da ya sani ba har alfijir ya bullo, ko kuma aka kira sallah, ko kuma suka ji an tayar da ikama, to sai mijin yai maza ya zare gabansa daga farjin matarsa. Shike nan azuminsu yana nan daram, kawai sai su yi wanka su ci gaba da azuminsu, matukar ba su ci gaba da saduwar ba bayan sun fahimci bullowar alfijir.
Amma bayan sun ji an kira sallah, kuma sun tabbatar da hudowar alfijir amma sai suka ci gaba da saduwarsu, to azuminsu ya karye. Don haka bayan Ramadan duk su biyun za su rama azumin wannan yinin, sannan kuma su yi kaffara kamar haka:
1. Ko su 'yanta baiwa/bawa (sai dai yanzu babu bayi).
2. Ko su yi azumi 60, idan ba za su iya ba, saboda wani uzuri na shari'a, to...
3. Sai su ciyar da miskinai (mabukata) guda 60.
4. Idan tsananin talauci ya sa ba za su iya ciyar da mutum sittin ba, to kaffarar ta saraya a kansu.
Wannan ita ce amsar da malamai suka bayar, kamar sheikh Bin Baaz da Sheikh Uthaimeen da sauransu.
Wallahu a'alam.
Gae neman karin bayani daga malamai, to ga abin da SHEIKH UTHAIMEEN R. Ya ce game da wannan mas'alar.
ﻭﺳﺌﻞ ﺍﻟﺸﻴﺦ عثيمين ﺭﺣﻤﻪ ﺍﻟﻠﻪ : ﺇﻧﺴﺎﻥ ﺣﺪﻳﺚ ﻋﻬﺪ ﺑﺎﻟﺰﻭﺍﺝ، ﻭﺃﺗﻰ ﺃﻫﻠﻪ ﻓﻲ ﺁﺧﺮ ﺍﻟﻠﻴﻞ ﻇﻨﺎً ﻣﻨﻪ ﺃﻥ ﺍﻟﻠﻴﻞ ﺑﺎﻕ، ﻭﺇﺫﺍ ﺑﺎﻹﻗﺎﻣﺔ ﺗﻘﺎﻡ ﻓﻤﺎ ﺗﻘﻮﻟﻮﻥ؟ ﻫﻞ ﻋﻠﻴﻪ ﺷﻲﺀ؟
ﻓﺄﺟﺎﺏ : " ﻻ ، ﻣﺎ ﻋﻠﻴﻪ ﺷﻲﺀ ، ﻻ ﺇﺛﻢ ، ﻭﻻ ﻛﻔﺎﺭﺓ ، ﻭﻻ ﻗﻀﺎﺀ ؛ ﻷﻥ ﺍﻟﻠﻪ ﺗﻌﺎﻟﻰ ﻗﺎﻝ : ( ﻓَﺎﻵﻥَ ﺑَﺎﺷِﺮُﻭﻫُﻦَّ ) ﺃﻱ : ﺍﻟﻨﺴﺎﺀ ( ﻭَﻛُﻠُﻮﺍ ﻭَﺍﺷْﺮَﺑُﻮﺍ ﺣَﺘَّﻰ ﻳَﺘَﺒَﻴَّﻦَ ﻟَﻜُﻢُ ﺍﻟْﺨَﻴْﻂُ ﺍﻷَﺑْﻴَﺾُ ﻣِﻦَ ﺍﻟْﺨَﻴْﻂِ ﺍﻷَﺳْﻮَﺩِ ﻣِﻦَ ﺍﻟْﻔَﺠْﺮِ ) ﺍﻟﺒﻘﺮﺓ .187/ ﻓﺎﻟﺜﻼﺛﺔ ﻛﻠﻬﺎ ﺳﻮﺍﺀ : ﻣﺒﺎﺷﺮﺓ ﺍﻟﻨﺴﺎﺀ ﻭﺍﻷﻛﻞ ﻭﺍﻟﺸﺮﺏ ، ﻭﻻ ﺩﻟﻴﻞ ﻋﻠﻰ ﺍﻟﺘﻔﺮﻳﻖ ﺑﻴﻨﻬﺎ، ﻛﻠﻬﺎ ﻣﻦ ﻣﺤﻈﻮﺭﺍﺕ ﺍﻟﺼﻴﺎﻡ، ﻭﺇﺫﺍ ﻭﻗﻌﺖ ﻋﻠﻰ ﻭﺟﻪ ﺍﻟﺠﻬﻞ ﺃﻭ ﺍﻟﻨﺴﻴﺎﻥ ﻓﻼ ﺷﻲﺀ " ﺍﻧﺘﻬﻰ ﻣﻦ " ﺍﻟﻠﻘﺎﺀ ﺍﻟﺸﻬﺮﻱ "
Dalibinku:
Bukhari Musa Adam
17/09/1440 = 22/5/19
May 24, 05:27 AM
Replies
(0)
×
Related Posts
Trending Discussions
friendship
wai please how do people get to have so much friends abin na bani mamaki I literally don't have any...
Read more
Relationship
Why is it that working class guys like me only meet idle ladies
I find it hard to understand why ladies that don't work or do business or have money wants to get ma...
Read more
Relationship
What is your opinion on Jigida?
What do u know about jigida??? I never use it but yanzu ta fara burgeni Ina so how do u think about...
Read more
General
A Message to My Princess (unknown wife)
Assalamu alaikum!
how are you doing my princess? first I would like to say I'm so sorry it's been 8...
Read more
Marriage
Me yake fara zuwan ranka idan kayi tunanin Aure?
Aduk Lokacin Da Kayi Tunanin Yin Aure Me Yake Fara Zuwa Ranka?
Marriage
Join the Discussion
Sign in to share your thoughts and engage with the community.
Login to Comment