HUKUNCIN YIN SALLAR NAFILA BAYAN WUTIRI!
:
𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
:
Assalamu alaikum malam, Allah ya kara maka basira, malam dan Allah tambayata a nan ita ce, ni ce na yi sallar Isha, na kuma yi Shafa'i da Wuturi, to kuma sai Allah ya ba ni ikon tashi cikin dare, shin Wuturi zan sake ko dukka zan sake?
:
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
:
Wa'alaikumus Salám, amin na gode bisa addu'o'iku na alheri. Babu laifi ga wanda ya yi wutiri a farkon dare ko a tsakiyar dare idan ya sake yin wata sallar nafila a daren a bayan wutirin nan nasa, sai dai abin da aka fi so shi ne mutum ya sanya sallarsa ta qarshen dare ta zama wutiri ne, saboda Abdullahi ɗan umar ya ruwaito cewa Annabi ﷺ ya ce: "Ku sanya sallarku ta qarshen dare ta zama wutiri".
Albukhariy (998), Muslim (751).
Amma wanda ya riga ya yi sallar wutiri, to idan ya sake yin wasu raka'o'in a bayanta ba zai sake maimaita wani wutiri daga baya ba. Saboda hadisi ya tabbata daga Dalq ɗan Aliyu ya ce: Na ji Manzon Allah ﷺ yana cewa: "Ba a wutiri biyu a dare ɗaya". Attirmizhiy (470), Annasá'iy (1679), Abu Dawud (1439).
Wato dai a taqaice idan mutum ya riga ya yi sallar wutiri sai kuma daga baya ya so ya yi sallar nafila a daren, to hakan ya halasta ba tare da wani karhanci ba, saboda umurnin da Annabi ﷺ ya bayar cewa a sanya sallah ta qarshe a dare ta zama wutiri, ba umurni ne na wajabci ba, umurni ne na mustahabbanci, sai dai kamar yadda bayani ya gabata, duk wanda ya yi sallar wutiri, kuma ya qara yin sallah a bayanta, to ba zai maimaita wani wutiri na biyu ba, kamar yadda hadisin can ya bayyana.
Dubi Almuhallá (2/91, 92), da Almajmú'u (4/16).
Allah S.W.T ne mafi sanin daidai.
Related Posts
Trending Discussions
friendship
wai please how do people get to have so much friends abin na bani mamaki I literally don't have any...
Read more
Relationship
Why is it that working class guys like me only meet idle ladies
I find it hard to understand why ladies that don't work or do business or have money wants to get ma...
Read more
Relationship
What is your opinion on Jigida?
What do u know about jigida??? I never use it but yanzu ta fara burgeni Ina so how do u think about...
Read more
General
Ya yanayin Sanyi a wajen ku at this time?
Aslm jama'a barkan mu d wannan rana da fatan kowa ya tashi lfy Allah yasa haka ameen..
jama'a ya yan...
Read more
General
Guys on this app wan make me crazy
Matchmaker
like why on earth will you be doing this we all know why we are here and u guys keep on doing silly...
Read more
Matchmaker
Your Birthday.
Meet your Twin by dropping your Date of birth, mine is 30th july. & yours...
Entertainment
Me yake fara zuwan ranka idan kayi tunanin Aure?
Aduk Lokacin Da Kayi Tunanin Yin Aure Me Yake Fara Zuwa Ranka?
Marriage
Join the Discussion
Sign in to share your thoughts and engage with the community.
Login to Comment