Matsalar saurin fushi (Anger issue)
Alhaji Hamza May 12, 11:25 AM

Matsalar saurin fushi (Anger issue) 1

Na dan jima ina ganin masu fama da matsalar saurin fushi wasu suce sun bi hanyoyi sun warke wasu Kuma su ce ba su warke ba. Ba a batun saurin fushi ba kadai, akan komai da yake lalura ce ta cikin jiki ko ta wajenshi; magani yakan bambanta Kuma ya ta'allaka da Imanin mai lalurar. Misali yawaita TA'AWIZI tabbas yana korar fushi, haka nan idan a tsaye ake sai a zauna..da dai sauran karashen shi ma magani ne sadidan. To amma sai mu tarar wani ya bi duk matakan amma shiru. A gaskiya rashin imaninmu na gaske da abin shi yafi zama sanadi da ba ma ganin tasirinshi. Haka nan ganin likitocin da abin ya shafar wanda da yawanmu a wannan zamanin mun fi yarda da ganin likitan asibiti sama da yin addu'a akan lalura (ba a hana neman magani ba) amma ni sai nake cewa; shi likitan asibiti sai yayi binkice nan-da-can, sannan ya bayarda maganin da yake da ran zai warke amma Allah da ake karanta sunayenShi da addu'a shi Yasan jikin domin shi Ya halicci jikin, kuma ciwon ikonShi ne, haka nan warakar, to na fi amince miShi. Allah Ya hore mana lafiya Ya hore mana Imani na gaskiya, amin
post

Replies

(9)
Meenah2 May 12, 02:28 PM
Amin ya rabbi jazakallh khair
reply 2
Alhaji Hamza May 12, 03:41 PM

Amin-amin
reply 1
Anonymous #1 May 12, 05:16 PM
Amin jazakallahu khair
reply 1
Alhaji Hamza May 12, 10:22 PM

amin-amin
reply 0
Anonymous #2 May 15, 08:06 AM
Masha Allah gaskia nikaina inada saurin fushi Ina samun waraka idan na dauko Qur'ani nayi tilawa
reply 2
Maman Haneef May 15, 12:31 PM
Amin Amin
reply 2
Mustapha Bashiru May 16, 08:49 AM

amin
reply 0
Shuaibu garba May 18, 05:41 AM
haka
reply 0

Related Posts


Trending

Wane course ne idan mutum yayi ze samu aiki General
how i feel about women General
Should i do it? she's tempting me Advice
friendship Relationship
Future Husband General
ga wanka ga sana'a ga 'ya chanji Amma Babu budurwa Allah yakawo nagari General
Are you ready!!! General
A Security guard at our school hmm!, wai he's in love with me Advice
Pure truth about women regarding marriage General
what do you do for fun? Entertainment
Why is it that working class guys like me only meet idle ladies Relationship
What would you like to eat this weekends? Food
I find it hard to approach ladies General
If I get married, I want to be very married Marriage
What do you plan to Achieve this week? Business
Help a sister Relationship